An shiga zaman makoki a Nijar | Siyasa | DW | 19.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An shiga zaman makoki a Nijar

Zanga-zangar ta adawa da gidan jaridar Charlie Hebdo na Faransa dai ta yi sanadin mutuwar akalla mutane goma yayin da mutane 173 suka samu munanan raunika.

Cikin irin abubuwan da aka sanyawa wuta sun hadar da makarantu na mabiya addinin Kirista da gidajen marayu da Kiristan kan lura da su a cewar Adily Toro, mai magana da yawun 'yan sandan kasar ta Nijar lokacin da ya ke bayani ga manema labarai a yau Litinin.

To ganin cewa Musulmi sun gudanar da wannan zanga-zanga a kasashen duniya da dama an kuma kammala ta lami lafiya to ko me ya jawo ta Nijar din ta munana, Moussa Changari mai fafutukar hakkin dan Adam ne a jamhuriyar ta Nijar:

"A wadansu kasashe ba a hana yin wannan zanga-zanga ba, amma a Nijar bayan da malamai a masallatan juma'a da kungiyoyi suka kira taron Allah Wadai hanasu aka yi aka kuma tura da sojoji. Kafin ranar ma minista ya fito ya yi barazana cewa zasu dau matakai na hana wannan zanga-zanga.

Duk da wannan barazana dai al'ummar kasar ta Nijar sun fita dan nuna kyamarsu ga irin zanen batanci da wannan jarida ta Faransa da ake kira Charlie Hebdo ta yi ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.W.A). Shiga kuma macin shugabannin wasu kasashen duniya da aka yi a birnin Paris da shugaban kasar ta Nijar Muhammadou Issoufou ya yi dan Allah wadai da 'yan bindigar da suka halaka ma'aikatan jaridarana ganin ya taka muhimmiyar wajen harzuka mazauna kasar ta Nijar da ke zama mai rinjayen Musulmi.

To ko ina aka kwana kan kyakkyawar dangantaka da ake ganin akwaita tsakanin Nijar din da Faransa? Anan ma Moussa Changari ya yi mana karin bayani.

"Wannan dangantaka da kake magana akai tsakanin kasashen akwaita amma ba wai ra'ayin al'umma ba, saboda shi ma shugaban kasa ya ce dan saboda wannan dangantaka da ke tsakanin kasashen ne yaje taron, wani ma zai ce zaman mu da Faransa zaman cuta ne suna cuta mana muna baya garesu"

Shi kuwa a nasa ra'ayin Dauda Tankama mataimakin shugaban kungiyar Kadet mai fafutukar kare Demokradiya a Nijar ya ce irin kalamai da shugaban kasar ta Nijar ya yi bayan kammala waccen ziyara da na ministan cikin gida na kan gaba wajen iza wutar zanga-zanga:

" Da ya zo aka yi masa tambaya sai ya ce shi shi ne Charlie kuma 'yan kasar Nijar ma su ma Charlie ne da yazo da wannan kalami mutane basu jadadi ba haka shi ma ministan cikin gida ya kara da kalaman tada hankali na hana a yi zanga-zangar ta karfin iko "

To baya ga neman kalamai na kwantar da hankulan 'yan kasa duk da cewa mutane da dama a jamhuriyar ta Nijar sun sha mamaki kan yadda aka samu wannan tashi hankali da ya yi sanadin rasa rayuka da kone-konen wajen ibadu da ma kadarori na mabiya addinin Kirista da suke zaman lafiya tare a ra'ayin Moussa Changari dole mahukunta su tashi tsaye wajen bada horo musamman ga matasa dan nuna juriya a yayin zaman tare da mabanbantan ra'ayoyi da addiniai uwa uba yin adalci a tsakanin al'umma.

"Horo ga jama'a da adalci idan babu a kowa ce kasa za a iya fuskantar tashin hankali"

Tuni dai mahukuntan wannan kasa suka bayyana zaman makoki na kwanaki uku daga yau Litinin saboda wadanda suka rasa rayukansu biyo bayan wannan zanga-zanagar kyamar zanen batanci na jaridar ta Cahrlie Hebdo da ke Faransa.

Sauti da bidiyo akan labarin