1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shawo kan gobarar daji a wajen Berlin

August 24, 2018

Jami'an kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar daji a jihar Brandenburg da ke wajen Berlin a Jamus.

https://p.dw.com/p/33it6
Waldbrände in Brandenburg
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Ma'aikatan kwana kwana sun shawo kan gagarumar wutar daji da ta kama a wajen Berlin.

Karl-Heinz Scroeter ministan cikin gida na jihar Brandenburg inda aka sami tashin gobarar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa a halin da ake ciki wutar ta lafa kadan. 

Gobarar ta mamaye wani wuri mai cike da itatuwa da yawa da ya kai fadin hecta 350. 

Ma'aikatan kashe gobara kimanin 600 ne suka dukufa aikin kashe gobarar.
 
Mataimakin shugaban gundumar Postdam-Mittelmark Christian Stein yace babban kalubalen da aikin kashe gobarar ya fuskanta shine nakiyoyi da ke binne a karkashin kasa wadanda basu fashe ba tun lokacin yakin duniya na biyu.

Kauyuka kimanin uku ne suka fuskanci barazanar gobarar wadda tun a daren Alhamis aka yi ta kokarin kwashe mutane fiye da 500 da lamarin ya shafa.