An sauya manya hafsoshin sojin Najeriya | Labarai | DW | 16.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sauya manya hafsoshin sojin Najeriya

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya tabbatar da sauyin manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar.

default

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan

Karkashin sabon sauyin dai Air Mashal Alex Badeh ne babban hafsan dakarun tsaron kasar inda ya maye gurbin Admiral Ola Sa'ad Ibrahim yayin da Manjo Janar Keneth Minimah ya canji Leftanar Janar Azubuke Ehijirika a matsayin sabon shugaban rundunar tsaron kasa ta kasar.

Real Admiral Usman Jibril ne dai shugaban ya nada a matsayin mutumin da zai jagoranci rundunar tsaron ruwa ta kasar, sai kuma Air Vice Marshal Adesola Amosu wanda ya zamo shugaban mayakan sama na kasar.

Najeriya dai na fuskantar barazanar tsaro kama daga ta 'yan kungiyar nan da aka sani da suna Boko Haram a arewa da kuma yan fashin teku a sashen kudancinta.

Mawallafi: Ahmed Salisu/Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman