An sanya dokar hana fita a Indiya | Labarai | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sanya dokar hana fita a Indiya

Mutane 30 sun mutu a zanga-zangar da ta barke a yankin Panchkula da ke arewacin kasar Indiya biyo bayan hukuncin kotu a kan wani malamin addini da aka samu da laifin yi wa wasu mata biyu fyade.

Daruruwan magoya bayan malamin sun gudanar da zanga-zanga a harabar kotun da ke a yankin Panchkula a arewacin kasar Indiya bayan da kotun ta sami malamin da laifin aikata fyade kan wasu mata biyu da mabiyansa ne, masu zanga zangar suna kalubalantar hukuncin kotun inda suka nuna bacin ransu ta hanyar kona motoci da wasu gine-gine a rikicin na wannan juma'ar, akwai wasu mutane fiye da dari daya da suka sami rauni a sanadiyar zanga-zangar.

'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa daruruwan magoya bayan malamin da suka fantsama a tituna garin, kotu ta sami Guru Ram Rahim mai shekaru hamsin da laifin yi wa matan biyu fyade a shekara ta 2002, tun wannan lokacin aka soma shari'ar da ba ta yi wa miliyoyin mabiya Gurun dadi ba, an zartas da hukuncin daurin shekaru bakwai akan Guru Rahim, kawo yanzu jami'an tsaro na kokarin shawo kan rikicin da ya jefa yankin cikin rudani, mai magana da yawun malamin addini ya yi kira ga jama'a da su kawo karshen boren don tabbatar da zaman lafiya, ganin munin lamarin ya sa gwamnati ta ayyana dokar hana fita a wannan yankin na wani lokaci.