An sanya dokar hana fita a Baltimore | Labarai | DW | 28.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sanya dokar hana fita a Baltimore

Mahukuntan birnin Baltimore na Amirka sun sanya dokar hana fita bayan barkewar tashin hankalin biyo bayan kisan wani bakar fata da 'yan sanda suka yi a wannan wata.

Mahukuntan sun kuma haramta wa mutane fita daga gidajensu har tsawon mako guda da nufin maido da doka da oda a birnin, kana sun yi Allah wadai da yadda wasu mutane suka yi amfani da tashin hankalin wajen lalata kadarorin mutane da kuma yin sace-sace.

Tashin hankalin na Baltimore dai ya fara ne bayan jana'izar Freddie Gray wanda ya rasu a hannun 'yan sanda, daidai lokacin da jama'a a kasar ke cigaba da muhawar kan yadda 'yan sanda ke amfani da karfi kan bakaken fata.

Nan gaba a wannan makon ne mahukuntan a birnin suka ce za su gudanar da bincike don gano wanda ke da hannu a tashin hankalin da nufin hukunta su kamar yadda doka ta tanada.