An sanar da ranar zaben ′yan majalisar Tchadi | Labarai | DW | 14.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sanar da ranar zaben 'yan majalisar Tchadi

Hukumar zabe ta kasar Tchadi ta sanar da ranar 31 ga watan Disambar bana a matasayin ranar gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, bayan kwashe shekaru biyar ana dage zaben sakamakon yawaitar ayyukan ta'addanci.

Zauren Majalisar mai ci a yanzu dai cike yake da magoya bayan shugaban kasar Idriss Deby wanda ke mulkin kasar tun 1990. A watan Janairun daya gabata ne gwamnatin kasar ta janye dokar ta bacin data sa a yankin Tibesti da Ouaddai da kuma Sila wadanda ke arewaci da gabashin kasar biyo bayan bankado wata ma'ajiyar makamai da sojojin kasar suka yi.

Jim kadan bayan fitowar wannan sanarwa daga hukumar zaben kasar ta Tchadi, wasu daga cikin jam'iyyun adawa suka bayyana amincewa da kuma jinjinawa mahukuntan kasar game da janye dokar ta bacin wacce ta haifar da tsaiko a harkokin gudanar da rayuwar al'umma.