An samu zabtarewar ƙasa a Japan | Labarai | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu zabtarewar ƙasa a Japan

Zabtarewar ƙasa ta hallaka kusan mutane 40 a ƙasar Japan

Kimanin mutane 36 da suka hada da yara sun hallaka sakamakon zabtarewar ƙasa bayan ruwan sama da aka sheka a yankin yammacin birnin Hiroshima na ƙasar Japan.'Yan sanda sun ce akwai yiwuwar samun ƙarin mutanen da abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da neman mutane bakwai da suka ɓace bayan faruwar lamarin. Masu aikin ceto sun yi amfani da jirage sama masu saukan ungulu domin kwashe mutanen da suka tsira.

Tuni aka tura da dakaru 500 domin aikin ceto, yayin da Firamnistan ƙasar ta Japan Shinzo Abe ya katse hutun da yake yi na lokacin bazara domin komawa Tokyo babban birnin ƙasar, domin tinkarar lamarin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane