1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu tsaiko a sasanta rikicin Libiya

January 14, 2020

An tashi a taron neman sansanta bangarori masu gaba da juna a Libiya da aka yi a kasar Rasha ba tare da Janar Khalifa Haftar ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita buda wuta da aka tsara ba.

https://p.dw.com/p/3W9uO
Kombibild - Putin, Khalifa Haftar, Fajis al-Sarradsch

Da fari dai ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ce kusan dukkanin masu jayayya da juna a rikicin kasar Libiya, sun sanya hannu kan yarjejeniyar ta tsagaita buda wuta, in banda madugun yakin Libiya Khalifa Haftar da kakakin daya bangaren majalisar dokokin Libiyar Aguila Saleh. Sai dai a karshe Khalifa Haftar ya fice daga kasar ta Rasha ba tare da ya sanya hannun ba, duk da sanarwar da Mr. Lavrov ya bayar na yiwuwar mutanen su sanya hannu kan yarjejniyar da safiyar Talata.

Madugun yakin na Libiya ya bukaci cimma wata bukata ce da ta shafi hannun Hadaddiyar Daular Larabawa. Sakataren harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce za dai a cimma matsaya kan wannan batu. Nan gaba cikin wannan watan na Janairu ne dai ake sa ran bangarorin masu jayayya da juna za su sake wani zaman a Berlin fadar gwamnatin Jamus.