An samu sauyin yanayin a shekarar 2013 | Labarai | DW | 09.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu sauyin yanayin a shekarar 2013

Hukumar kula da yanayi da kuma bincikken sararin samaniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya OMM ta ce duniya na fuskantar gurɓacewar muhali.

Hukumar ta ce yawan sinadari na hayaƙi mai iskan guba na gas da ya tuɗaɗa a cikin sararin duniya da kuma cikin teku wanda ɗan Addam ke shaƙa ya wucce kima a shekara da ta gabata.

A cikin wani rahoto na shekara da hukamar ta bayyana a yau, babban sakataran hukumar Michel Jarrau. Ya ce suna da tabbas kan cewar yanayi na canzawa ne saboda halayar ɗan Addam ta hanyar yin amfanin da wasu abubuwan da kan janyo gurɓacewar muhali.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu