An samu jami′in gwamnati da laifi | Labarai | DW | 13.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu jami'in gwamnati da laifi

Mahukuntan Koriya ta Arewa sun aiwatar da hukuncin kisa ga wani jigon gwamnati

Mahukuntan kasar Koriya ta Arewa sun tabbatar da aiwatar da hukuncin kisa kan daya daga cikin jiga-jigan gwamnatin kasar Jang Song Thaek, wanda kafin wannan lokacin ya ke da karfin fada aji.

Marigayi Jang Song Thaek kawu ne ga Shugaba Kim Jong-Un, kuma kamfanin dillancin labaran kasar ya ce, marigayin ya zama maciyin amana na kin karawa. A wannan Alhamis da ta gabata aka yanke tare da aiwatar da hukuncin ga Jang. Wata kotun soja ta musamman ta same shi da duk laifun da aka tuhume shi, da suka hada da safarar miyagun kwayoyi da zagon kasa wa jam'iyya mai mulki da kuma neman kifar da gwamnati.

Tun cikin watan jiya kafofin leken asirin Koriya ta Kudu suka ruwaito cewa an tunbuke Jang Song Thaek daga duk mukaman gwamnati da yake rike da su a kasar ta Koriya ta Arewa mai gudanar da lamura cikin sirri.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar