1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu fashewa a birnin Berlin na Jamus

Suleiman BabayoMarch 15, 2016

Mutum daya ya hallaka sakamakon fashewa da aka samu a birnin Berlin fadar gwamnatin kasar Jamus inda jami'an tsaro ke gaba da bincike.

https://p.dw.com/p/1IDSB
Deutschland Auto explodiert in Berlin
Hoto: DW/N. Jolkver

'Yan sanda a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus suna bincike kan fashewar da aka samu a cikin wata mota da matukin motar da rasa ransa. Bayan killace yanki babu wani abin fashewa da jami'an tsaro suka sake ganowa.

Fashewar ta faru da karfe 8 na safe lokacin da ake tururuwar zuwa wajen aiki. Tuni masu binciken sun gano mutumin da ya hallaka amma sun bayyana sunansa saboda binciken da ake ci gaba da yi.