An samu ci-gaba kan yaki da Ebola a Saliyo | Labarai | DW | 22.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu ci-gaba kan yaki da Ebola a Saliyo

Hukumomin kasar Saliyo sun ce suna ganin haske a kokarin da suke na yaki da cutar Ebola, bayan da suka tsaurara bincike cikinn gidajen al'umma

Kwanaki uku aka yi ana bincike, tare da fadakar da al'ummar ta saliyo a cikin gidajensu ba tare da sun fita waje ba, wanda kuma hakan ya sa an gano wasu mutanen da dama da suka rasu sakamakon cutar, da kuma wadanda suke dauke da cutar ta Ebola. A kasar Laberiya mai makwabtaka da kasar ta Saliyo inda kuma nan ne aka fi samun mafi yawan mace-macen na Ebola, an buda wata sabuwar cibiyar kula da masu cutar inda nan take aka kawo marasa lafiya a kalla 105 bayan bincike aka gano 56 daga cikin su na dauke da cutar ta Ebola a cewar Ministan kiwon lafiyar kasar Tolbert Nyensuah.

A hannu daya kuma wani limamin Coci na darikar Katolika dan kasar Spain kuma mai shekara 69 da haihuwa, ya kamu da cutar ta Ebola a kasar Saliyo wanda tun a daran jiya aka fuce da shi ya zuwa birnin Madrid kuma yana cikin mawuyacin hali. Kawo yanzu dai a kalla mutane 2,793 ne suka rasu sakamakon wannan cuta daga cikin mutane 5,762 da suka kamu da cutar a cewar hukumar lafiya ta duniya WHO.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo