1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu bullar Ebola a Port Harcourt

August 31, 2014

Hukumomin lafiya a jihar Rivers ta Najeriya, sun tabbatar da bullar cutar Ebola a Port Harcout, inda bincike ya tabbatar da kamuwar wata mata da wannan ciwo.

https://p.dw.com/p/1D4N4
Kind mit Ebola in Kailahun Sierra Leone 15.08.2014
Hoto: Carl De Souza/AFP/Getty Images

Wadda ta kamu da wannan cuta dai ta Ebola, itace matar likitan nan da ya rasu sakamakon kamuwa da cutar inda tun wannan lokaci aka soma gunadar da bincike kan matar sa. Ministan kiwon lafiya na jihar ta Rivers Sampson Parker ne ya tabbatar da wannan labari a yau din Lahadi, inda yace tuni wasu mutane guda uku da suka samu mu'amala da wannan mata na kalkashin kulawar likitoci a wani asibiti na musamman dake wajan garin domin tantance lafiyar su.

Shi dai wannan Likitan mai suna Ike Enemuo, da aka bayyana rasuwar sa a ranar Juma'a da ta gabata, shine na shidda daga cikin wadanda suka mutu sakamon cutar a Najeriya, inda matarsa wadda ita ma babbar likitace ta kamu da wannan cuta. Daga cikin mutane 15 dake dauke aka samu dauke da cutar a Najeriya, 7 sun samu warkewa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu