1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami harbe-harbe a Bayelsa

Muhammad Bello MA
September 30, 2019

Wani yamutsi da ya auku a zauren majalisar jihar ne ya yi sanadin sanar da wani Kakaki bayan arcewar da mai rike da mukamin ya yi a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/3QVsB
Nigeria Polizei in Lagos
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Rahotanni daga Bayelsa da ke yankin kudancin Najeriya, na cewa an ji karar harbe-harbe a majalisar dokokin jihar bayan wani yamutsi da aka samu lokacin da ake kokarin tsige kakakin majalisar.

Jami’an tsaro ne dai suka yi ta harbe-harben a cewar rahotannin, sakamakon tsananin rudanin da ya kaure a zauren majalisar a wannan Litinin.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu na yankin Nija Delta a Najeriyar, Muhammad Bello cewar 'yan majalisar na kokarin tsige kakakin majalisar ne ya haddasa harbe-harben.

Koda yake Kakakin majalisar da za a tsige din ya arce da sandar majalisar, 'yan majalisar sun tsige shi sun dora sabo, a cewarsa.