An sami ci gaba a tattaunawa kan Nukiliyan Iran | Labarai | DW | 21.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami ci gaba a tattaunawa kan Nukiliyan Iran

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce an sami ci gaba a tattaunawar da ake yi kan Nukiliyar kasar Iran.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce an sami ci gaba a tattaunawar da ake yi kan Nukiliyar kasar Iran.

Mr. John Kerry wanda ya bayyana hakan a yau Asabar, ya ce za a sake zaman cimma matsayin kwarai kan batun a makon gobe.

Ya kuma ce akwai wani zaman da manyan kasashen Turai za su yi yau Asabar a birnin London na kasar Burtaniya, sai kuma a koma birnin Laussane na kasar Swizaland a makon na gobe don cimma matsaya kan wanna batu.

Tun farko dai an jiyo shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran na cewar an dai sami bambancin ra'ayi a zaman da su ka yi a birnin Lausanne, sai dai a cewarsa ana iya cimma daidaito da manyan kasashen yamma kan takaddamar mallakar Nukiliyar kasar ta sa.