1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori ministan kudi kan badakalar cin hanci

Ramatu Garba Baba
November 14, 2022

Shugaba Akufo-Addo ya kori karamin ministan ma'aikatar kudin kasar Charles Adu Boahen daga aiki, a kan badakalar cin hanci a masana'antar hakar zinare.

https://p.dw.com/p/4JVAg
Ghana Präsident Nana Akufo-Addo mit Maske
Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya sallami karamin ministan ma'aikatar kudin kasar daga bakin aiki, wannan na zuwa ne bayan da aka bankado wasu takardu da ke nuna yadda Mr Charles Adu Boahen ke da hannu dumu-dumu a badakalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye masana'antar hakar zinaren kasar.

Shugaban ya sanar da korar ministan ne a wannan Litinin din tare da bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin na cin hanci da rashawa.

Ana ganin matakin ba ya rasa nasaba da yunkurin shugaban na ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa, tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki sun matukar fusata 'yan Ghana, har ta kai aka soma zanga-zangar neman shugaban kasar ya sauka daga kan karagar mulki a sakamakon matsin tattalin arziki da al'ummar kasar ta tsinci kai.