1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta sallami tsohon shugaban Chadi daga gidan yari

Abdoulaye Mamane Amadou
April 7, 2020

Gwamnatin Senegal ta sallami tsohon dan mulkin danniyar nan na Chadi kuma tsohon shugaban kasar Hissène Habré daga gidan yari har na tsawon watanni biyu a wani yunkuri na hana shi kamuwa da Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aZKW
Hissene Habre vor Gericht
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Tun daga farko dai kotun kasar ta Senegal inda tsohon shugaban kasar ta Chadi yake tsare, ta ce lauyan da ke kare Hissène Habré ya shigar da wata bukatar bayar da belinsa a gabanta, duba da yanayinsa na shekaru da kuma yadda yake iya harbuwa da kwayar cutar Coronavirus a gidan yarin da yake tsare a birnin Dakar, bukatar da kuma ta amince da ita. Mai shekaru  78 a duniya Hissène Habre, A wani zamanta na musamman a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2016, kotu ta kama shi da laifin aikata kisan kiyashi ne a kasar Chadi bayan ya yi mulki irin na kama karya a shekaru 1982 zuwa 1990, inda ake zargin mutane fiye da dubu 40 sun hallaka.