An sallami babban jami'in 'yan sanda na birnin Cologne a Jamus | Labarai | DW | 08.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallami babban jami'in 'yan sanda na birnin Cologne a Jamus

Mahukuntan Jamus sun dauki matakin dakatar da babban jami'in 'yan sanda na Cologne sakamako cin zarafin mata da aka samu a birnin lokacin bikin shiga sabuwar shekara.

An bayyana dakatar da Wolfgang Albers babban jami'in 'yan sanda na birnin Cologne daga bakin aiki saboda gaza kare mata lokacin bikin shiga sabuwar wannan shekara ta 2016. Albers dan shekaru 60 da haihuwa an yi masa ritaya na wani lokaci. Mahukuntan Jihar North Rhine Westphalia suka bayyana matakin a wannan Jumma'a.

'Yan sanda sun fuksanci suka bisa yadda suka gaza kare mata fiye da 120 wadanda aka ci zarafinsu lokacin bukukuwa na shiga sabuwar shekara a birnin na Cologne. Ana zargin maza daga yankin Gabas ta Tsakiya gami da kasashen arewacin Afirka da aikata laifin. Tuni aka cafke fiye da mutane 30 kuma kusan 20 daga ciki sun kasance 'yan gudun hijira da bakin haure masu neman mafaka. Lamarin ya janyo musanyen ra'ayi mai zafi cikin kasar ta Jamus bayan shigar kimanin bakin haure da 'yan gudun hijira milyan daya a shekarar da ta gabata ta 2015.