An sallami babban hafsan sojan Sudan ta kudu | Labarai | DW | 24.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallami babban hafsan sojan Sudan ta kudu

Yayinda rikicin 'yan tawaye da gwamnati ke kara rincabewa, hukumomi a Juba sun yi wa rundunar sojan kasar garan bawul

Südsudan Bor Militär 18.1.2014 General James Hoth Mai

James Hoth Mai da aka sallama

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya sallami babban hafsan sojojin kasar, bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa 'yan tawaye sun samu nasarar kwace rijiyoyin mai da ke arewacin kasar. Ba a dai bada dalilin koran janar James Hoth Mai, sai dai kawai gidan talabijin na gwamnati ya sanar da cewa an maye gurbinsa da Janar Paul Malong. To amma ana kyautata zaton ran shugaban kasa ya baci, bisa koma bayan da rundunar sojan kasar ke samu, a yakinsu da 'yan tawaye masu goyon bayan Riek Macher, wanda har ta kai yanzu aka fatattakin sojan gwamnati daga rijiyoyin man kasar mafiya girma.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal