An salami Malala Yousufzai daga asibiti | Labarai | DW | 04.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An salami Malala Yousufzai daga asibiti

Bayan watannin biyu da rabi na jinya a Ingila sakamakon harbi a ka da yan taliban suka yi ma ta a Pakistan likitoci sun ce ta yi dama so sai

Matashiyar yar kimanin shekaru15 wacce ke goyon bayan tsarin illimintar da yan mata, an kwantar da ita ne a asbitin Queen-Elizabeth Hospita dake a Birmingham a tsakiyar kasar Ingila.

A cikin wata sanarwa da likitocinta suka baiyana sun ce ya zuwa yanzu jiginta yayi dama so sai; kafin a sake yi mata wani aikin tiyata a cikin sabon watan mai shirin kamawa.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne yan ƙungiyar Taliban suka harbi yariyar a wani harin da aka kai akan wata motar bus ta yan makaranta a garin Swat da ke a yankin arewa maso gabashin Pakistan ɗin.

Mawallafi : Abdourahamane
Edita : Umaru Aliyu