An sako ′yan Bamenda 21 da suka yi bore | Labarai | DW | 10.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako 'yan Bamenda 21 da suka yi bore

Hukumomin Kamaru sun sako wasu mutane 21 da ke amfani da Ingilishi da ta kama a Bamenda a watan da ya gabata sakamakon zanga-zangar da suka gudanar.

Gwamnatin Kamaru ta sako matasa 21 da take tsare da su tun watan Disemba sakamakon shiga boren da 'yan kasar da ake amfani da Ingilishi suka yi a Bamenda don yi tir da mayar da su saniyar ware da bangaren Faransaci ke yi. Gidan rediyon kasar ya bayyana matakin da wani yunkuri na neman sulhunta rikicin cikin ruwan sanyi. Dama dai kungiyoyin kodago na malamai da lawyoyin da ke amfani da Ingilishi sun fice daga zauren tattaunawa har sai an sako wadanda aka kama.

Tun watannni biyun da suka gabata ne dai jihohin Kamaru biyu da ka amfani da Ingilishi suke gudanar da zanga-zanga da yajin aiki da nufin tilasta wa hukumomi yin daidai-wa-daida da takwarorinsu da ke amfani da Faransanci. Yanzu haka dai kusan komai ya tsaya cik a jihohin Arewa maso yammaci da kuma Kudu maso yammacin kamaru sakamakon yajin aikin gama gari da ke gudana a yanki. Kashi 20 cikin 100 na 'yan kamaru ne dai ke amfani da Ingilishi.