An sako wani ɗan ƙasar Jamus da aka sace a Najeriya | Labarai | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako wani ɗan ƙasar Jamus da aka sace a Najeriya

An sako mutumin wanda aka sace a makon jiya a Ogun da ke a yanki kudu maso yammacin Najeriya.

An ba da rahoton cewar wani ɗan ƙasar Jamus wanda wasu 'yan bindiga suka sace a makon jiya a jihar Ogun a yankin kudu maso yammacin Najeriya an sakoshi.

Kamfanin Julius Berger wanda a nan mutumin yake aiki ya sanar da cewar an sako ma'aikacin nasa salin alin. Sai dai kuma kamfanin mai yin aikin gine-gine a Najeriya bai bayar da arin haske ba a game da yadda aka ako mutumin.