An sako turawa da akayi garkuwa da su a Najeriya | Labarai | DW | 27.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako turawa da akayi garkuwa da su a Najeriya

A Najeriya,yan aware na yankin Naija Delta sun sako maaikatan kanfan9in mai 3 da suke garkuwa da su,Amurkawa 2 da dan kasar Burtaniya daya.

Kakakin gwamnati,Abel oshevere ya fadawa kanfanin dillancin labari na AFP a yau cewa,an mika mutanen 3 ga hannun jamian gwamnati a Warri,inda ya baiyana cewa suna nan cikin koshin lafiya.

Mutanen 3 suna cikin wasu turawa 9 ne da yan aware na Naija Delta suka sace a ranar 9 ga watan fabrairu,sauran 6 tuni an sake su bayan mako daya da sace su.