An sako shugaban adawar Uganda | Labarai | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako shugaban adawar Uganda

Wata babbar kotu a kasar Uganda ta bayar da umarnin sakin shugaban adawar kasar wato, Kizza Besigye.

Kotun da dauki wannan matakin ne bayan data ce , ci gaba

aba da tsare madugun adawa na kasar ya saba da dokokin kasar.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa kafin bayar da wannan umarni na yau, Kizza Besigye ya kasance a tsare ne tun daga biyu ga watan disambar bara kawo yanzu.

An dai tsare madugun adawar ne bisa laifuffuka da ake zargin sa da aikatawa da suka shafi cin amanar kasa da mallakar makamai ba bisa ka´ida ba a hannu daya kuma da yiwa wata mace fyade.

Rahotanni sun shaidar da cewa jim kadan da sakin sa, Kizza Besigye ya wuce kai tsaye ne izuwa gabashin kasar don ci gaba da gudanar da kamfe din yakin neman zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 23 ga watan fabarairun wannan shekara da muke ciki.

Ya zuwa yanzu dai Kizza Besigye na a matsayin babban mai adawa da shugaba Yoweri Museveni a neman wannan kujera mai alfarma ta kasar a lokacin wannan zabe mai zuwa.