An saki ′yan jaridar Spain da aka sace a Siriya | Labarai | DW | 30.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki 'yan jaridar Spain da aka sace a Siriya

Rahotannin da ke fitowa daga ƙasar Siriya na cewar an saki 'yan jaridar ƙasar Spain ɗin nan da aka sace cikin watan Satumbar shekarar da ta gabata.

Jaridar El Mundo wanda 'yan jaridar biyu ke yi wa aiki ce ta tabbatar da sakinsu nasu kuma ta ce tuni aka miƙa su ga sojin Turkiya wanda suka fafutuka wajen ganin an maida su gida.

Wata ƙungiya kamar yadda jaridar ta shaida, ta masu tsaurin kishin addini ce da ke da rassanta a Siriya da Iraki ta kame 'yan jaridar kuma ta yi garkuwa da su daidai lokacin da suke ƙokarin tsallaka kan iyakar Siriya da Turkiya bayan da suka kammala wani aiki na makonni biyu a birnin Raqqa da ke Siriya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abourahamane Hassane