An saki Saif al-Islam daga yarin Zintan | Labarai | DW | 11.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki Saif al-Islam daga yarin Zintan

Bayan shafe shekaru kusa shida a gidan yarin Zintan bisa zargin ruruta wutar rikicin Libiya, masu tayar da kayar bayan kasar sun saki Saif al-Islam dan marigayi Muammar Gaddafi.

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Libiya ta sanar da cewa ta saki Saif al-Islam dan tsohon shugaban Libiya marigayi Muammar Gaddafi daga gidan yarin birnin Zintan bayan yi masa afuwa. Shi da Saif al-Islam da ke zama da na biyu ga marigayin, an zata shi zai gaji mahaifinsa a kan kujerar mulkin Libiya. Amma kuma rikicin da kasar ta yi fama da shi ya sa wata kotu a birnin Tripoli yanke masa hukuncin kisa, amma kuma kungiya masu tayar da kayar baya ta ki mikashi.

Majalisar dokokin kasar Libiya da ke da cibiya a gabashin birnin Tobruk ce ta yi afuwar gama gari da Saif al-Islam Gaddafi ya ci gajiya. Sai dai kotun ICC da ke hukunta manyan laifukan yaki na ci gaba da nemansa ruwa a jallo bisa zargin aikata munanan laifuka lokacin da mahaifinsa Muammar Gaddafi ya yi yunkurin murkushe masu neman sauyi.

A watan Nuwamban 2011 aka kama Saif al-Islam mai shekaru 44 da haihuwa bisa zargin ruruta wutar rikicin kasar Libiya da kuma bada umurnin kashe masu zanga-zangar neman sauyi. Sai dai har yanzu babu wata majiya ta gwamnatin Tripoli da ta tabbatar da sakin nasa.