An saki masu zanga-zanga a Kwango | Labarai | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki masu zanga-zanga a Kwango

Hukumomi a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango sun sallami wasu mutane 20 da aka kama daga cikin masu zanga-zanga a wannan birni.

Babbar jam'iyar adawa a wannan kasa ta UDPS, da kuma jam'iya ta uku ta UNC da ke bangaran adawar ne dai suka yi kira ga wani zaman dirshan a harabar ofishin jami'an Majalisar Dinkin Duniya na Monusco da ke birnin na Kinshasa. Hakan kuwa na da burin neman buda tattaunawa ta kasa tsakanin bangarorin kasar, kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma ta birnin Addis Ababa na kasar Habasha a watan Fabrairu na 2013 ta tsaida wadda kasar ta Kwango ta sa ma hannu, dan ganin an kawo karshen tashe-tashen hankulla da ake fuskanta a gabashin kasar na tsawon shakaru da dama. Daga nashi bangare Vital Kamerhe, jagoran jam'iyar UNC ya ce su basa bukatar a kai ga abubuwan da suka wakana a Burkina Faso, domin akwai yanyoyin kauce wa hakan, inda ya ce suna bukatar zaman tattaunawa na-gari tare da gwamnati don share hanyar zuwa ga zabe mai inganci a wannan kasa.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita : Umaru Aliyu