An saki jami′an Turai a Ukraine | Labarai | DW | 29.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki jami'an Turai a Ukraine

'Yan awaren Ukraine sun sake jami'an saka ido na kasashen Turai

'Yan awaren gabashin kasar Ukraine masu goyon bayan Rasha sun sake rukuni na biyu na masu saka ido daga kungiyar tsaro da hadin kai ta kasashen Turai. Mutanen maza uku da mace daya, an yi garkuwa da su tun karshen watan Mayu, kuma jiya Asabar aka sake su. Ga duk alamu suna cikin koshin lafiya.

Tun farko Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira na neman sakin mutanen. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yaba da rawar da Rasha ta taka wajen sakin jami'an. Ranar Jumma'a da ta gabata, Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya tsawaita tayin ahuwar da ya yi wa tsageru masu dauke da makamai, duk da sabon tashin hankali da aka samu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar