An saki dan Faransa da aka sace a Kamarun | Labarai | DW | 31.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki dan Faransa da aka sace a Kamarun

Hukumomi sun tabbatar da sakin bafaranshen nan da aka sace a karshen watan Novemba a arewacin Kamarun

François Hollande shugaban Kasar ta Faransa ne ya sanar da cewa, an saki Limamin cocin nan dan kasar ta Faransa da aka kama tun ranar 31 ga watan Novemba da ya gabata a kusa da iyakar Najeriya da Kamarun.

Limamin cocin mai suna Georges Vandenbeusch dan shekaru 42 da haihuwa, an sace shi ne a cikin yankin da aka taba dauke dan kasar Faransar nan Moulin-Fournier da iyalin sa cikin watan Febreru, kuma aka sake su bayan watanni biyu.

Cikin wani jawabi da ya yi, shugaban kasar ta Faransa François Hollande ya isar da godiyar sa ga shugabannin kasar Kamarun da na Najeriya, da suka sa hannun har aka samun cimma sakin Limamin cocin.

Ministan harkokin wajan kasar Faransa Laurent Fabius zai isa Yaounde babban birnin kasar ta Kamarun domin tarbon Limamain cocin, dan tahowa da shi ya zuwa Kasar sa ta Faransa ba tare da bata lokaci ba. Kawo yanzu dai yan kasar Faransa guda shidda ne ke tsare a kasashen Malie da Siriya.

Mawallafi. Salissou Boukari

Edita. Usman Shehu Usman