An saki Abu Qatada | Labarai | DW | 13.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki Abu Qatada

Shehin malamin addinin na ƙasar Jodan Abu Qatada an sako shine bisa umarnin kotu ,daga wani gidan kurkun da ake tsare da shi a tsakiyar ƙasar Ingila cikin tsatsauran matakan tsaro

Abu Qatada wanda ɗan asilin ƙasar Jodan ne wanda sunansa na ainafi shine, Umar Othman an sako shi akan wasu tsatsauran sharuda da ke taƙaita masa fita, da yin tafiye tafiye.

Bayan da ya samu nasara a ɗaukaka ƙaran da ya yi akan yunƙurin da Brutaniya ta ke yi kusan shekaru goma, na neman tusa ƙesarsa zuwa ƙasar Jordan, inda zai sake fuskantar shara'a akan zargin da ake yi masa na shirya wani harin ta'addanci.Ƙasashen Jordan da Brutaniya na nuna addawa da wannan hukumcin wanda Brutaniya ta ce zata ƙalubalance shi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu