An sake zaben Zimbabwe a hukumar UNHCR | Siyasa | DW | 28.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An sake zaben Zimbabwe a hukumar UNHCR

Kasar Zimbabwe ta sake samun wakilcin shekaru uku a hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD

Kofi Annan

Kofi Annan

Kujeru hudu ne aka ware wa kasashen Afurka a hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD, wadda sakatare-janar Kofi Annan ke fatan ganin an dakatar da ayyukanta a wannan shekara, sakamakon sabanin da ake yi akanta. Wakilin kasar Amurka a hukumar William Brencick ya ce kasarsa ta ji haushi da takaicin shawarar sake zaben kasar Zimbabwe da kasashen Afurka suka tsayar duk da takunkumin da Amurka da kawayenta na nahiyar Turai suka aza akan shugabanta Robert Mugabe. Bisa ga ra’ayin gwamnatin amurka kasar Zimbabwe na karkashin mulki ne na danniya da kama karya da take hakkin dan-Adam, inda ‚yan adawa ke cikin hali na zaman dardar. An ji daga bakin wani dan majalisar dattijan kasar Amurka yana cewa zaben kasar Zimbabwe a wannan hukuma, bacin suna ne, da kuma mayar da hukumar kamar wani abin ba’a. An ji irin wannan korafin daga mataimakin wakilin kasar Australiya a MDD Peter Tesch, wanda ya kara da cewar zaben Zimbabwen da aka yi ya zama kyakkyawan misali a game da lalacewar ayyukan hukumar baki daya. Kawo yanzun dai kasar Birtaniya ba ta ce kome ba, sai dai kawai cewar kowa ya san matsayinta a game da Zimbabe. A mayar da martani game da haka wakilin Zimbabwe a MDD Boniface Chidyausiku ya ce duk wanda ke zaune a cikin wani gida na gilashi to bai kamata ya nemi da a yi wasan jifa da shi ba. A cikin shawarwarin canje-canje da sakatare-janar Kofi Annan ya bayar a farkon wannan shekara, ya nemi da a canza tsarin hukumar, inda za a nada wani kwamitin rikon kwarya, wanda zai rika bin diddigin manufofin hakkin dan-Adam a kasashen dake da wakilci a hukumar. Annan ya ce a yanzu an shiga wani hali ne, inda martabar hukumar ta kare hakkin dan-Adam ta MDD UNHCR ke zubewa a idanun jama’a. Sauran kasashen da aka zabesu a hukumar sun hada da Argentina da Autraliya da Azerbaijan da Bangladesh da Botswana da Brazil da Kamaru da China da Jamus da Japan da Moroko da Amurka da kuma Venezuela.