An sake zaban Al-Jafari a mukamin firaministan Iraki | Labarai | DW | 12.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake zaban Al-Jafari a mukamin firaministan Iraki

Kawancen jam´iyun ´yan shi´a da ke mulki a Iraqi sun sake nada FM mai ci Ibrahim al-Jafari ya yi tazarce a wannan mukami bayan nasarar da suka samu a zaben ´yan majalisar dokokin kasar. Al-Jafari ya kada abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Adel Abdul Mahdi da kuri´a daya kwal. Wannan kuri´a ta biyo bayan cece-kuce da aka shafe makonni ana yi abin da ya jinkirta yin shawarwarin kafa sabuwar gwamnati a Iraqi. A wani labarin kuma lauyoyin dake kare tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein sun karyata rahotannin da aka bayar cewa yana shirin shiga yajin cin abinci. A gobe za´a koma zaman shari´ar da ake masa, to amma lauyoyinsa sun ce zai kauracewa shari´ar har sai an sauke sabon alkalin kotun Ra´uf Rashid Abdul-Rahman daga wannan mukami na alkalin kotun.