An sake sanya Benazir Bhutto cikin ɗaurin talala na tsawon mako guda | Labarai | DW | 13.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake sanya Benazir Bhutto cikin ɗaurin talala na tsawon mako guda

An sake yiwa tsohuwar FM Pakistan Benazir Bhutto daurin talala a wannan karo na tsawon mako guda. Jami´an tsaro sun yiwa gidan da take a birnin Lahore na gabashin kasar, kofar rago sannan shaidu sun ce an girke ´yan sanda kimanin dubu 1 a kusa da ginin. Jami´ai a birnin Islamabad suka nunar, hukumomin Pakistan sun ba da umarnin hana Bhutto fita har tsawon kwanaki 7 don kare lafiyarta daga barazanar da ake yi na halaka ta. To amma magoya bayanta sun ce an dauki matakin ne don hana ta jagorantar wani maci da za´a yi na don nuna adawa da dokar ta baci da shugaba Pervez Musharraf ya kafa kwanaki 10 da suka wuce. A jiya daddare wani taron kasashen kungiyar Komonwelf a birnin London ya sake yin barazanar dakatar da Pakistan daga kungiyar mai membobi kasashe 53 har sai an dage dokar ta baci kafin ranar 22 ga watannan na nuwanba.