An sake samun cutar Polio a Najeriya | Labarai | DW | 05.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake samun cutar Polio a Najeriya

Sababbin wadanda aka samu da cutar Polio sun janyo koma baya a yaki da cutar cikin Najeriya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar da cewa an gano bullar kwayar cutar Polio karo na uku a Najeriya. Ana danganta rashin nasarar kakkabe cutar daga Najeriya da rikicin Boko Haram, saboda yaro na uku da aka gano yana dauke da cutar yana cikin yankin da dakarun gwamnati suka kwato daga hannun mayakan kungiyar ta Boko Haram. Sannan biyu daga cikin masu dauke da cutar suna wani sansanin 'yan gudun hijira da ke karkashin kulawar sojojin Najeriya. Hukumar Lafiya ta Duniyar ta ce cutar ta Polio ta kwashe shekaru biyar tana yaduwa a jihar Borno da ke fama da rikici mai nasaba da tsagerun Boko Haram tun shekara ta 2009.