An sake kashe mutane biyu a sabon fada tsakanin Hamas da Fatah | Labarai | DW | 27.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kashe mutane biyu a sabon fada tsakanin Hamas da Fatah

Kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna sun ci-gaba da fafatawa a kusa da jami´ar Islamiya ta magoya bayan Hamas dake Zirin Gaza, inda aka kashe akalla mutane 2. Hakazalika wasu ´yan bindiga sun yi garkuwa da jami´ai 4 na wata rundunar tsaro mai biyayya ga kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. A cikin daren jiya wani dan sanda na kungiyar Hamas ya cika sakamakon raunin da ya samu. Mutuwar sa ta sa yanzu yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka yi a jiya juma´a ya zuwa mutane 16. Tashe tashen sun sa a tilas an dakatar da tattaunawar kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa da ake yi tsakanin Fatah da gwamnatin Hamas.