1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kadammar da hari kan sojin Nijar

March 8, 2020

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne, sun tafka ta'asa a sansanin soja da ke yankin Diffa a kudancin Jamhuriyar Nijar. Maharan sun afka musu ne a Chetima Wangou.

https://p.dw.com/p/3Z3vf
Symbolbilder Niger Armee
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan sabon harin ya haddasa fargabar asarar mayaka, wanda ke zuwa bayan wasu jerin hare-hare da Nijar din ta gani a baya-bayan nan da suka yi sanadin mutuwar dakarun Nijar.

Shaidu sun ce harin da aka kaddamar kan sansanin Shetima Wangou, mayakan na tarzoma sun yi hakan ne bayan shigar wajen da suka yi cikin jerin gwanon motoci dauke da manyan mamakai.

Wasu majiyoyi na asibitin yankin sun tabbatar da labarin, sai dai ba su bayyana adadin asarar rayuka da aka yi ba.

Shetima Wangou dai waje ne da ke da nisan kilomita 25 da garin na Diffa.