An sake halaka wani mai adawa da Syria a birnin Beirut na Lebanon | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake halaka wani mai adawa da Syria a birnin Beirut na Lebanon

Kwamitin sulhun MDD ya yi tir da harin bam da aka kai yau a birnin Beirut wanda ya halaka akalla mutane 5 ciki har da wani dan majalisar dokoki mai adawa da kasar Syria, Antoine Ghanem. Lokacin da yake magana a matsayinsa na shugaban kwamitin sulhu a wannan wata, jakadan Faransa a MDD Jean-Maurice Ripert ya yi tir da harin bam yana mai cewa wani yunkuri ne na haddasa rudami a Lebanon a cikin wannnan lokaci mai muhimmanci. Nan da kwanki kalilan za´a gudanar da shugaban kasa a Libanon. Shi dai Antoine Ghanem wanda dan jam´iyar Falange ne ya rasa ransa ne hade da wasu mutane 4 a wani harin bam da aka kai da mota a wata unguwar Kiristoci da ke gabashin Beirut. A cikin shekaru biyu da rabi da suka wuce birnin Beirut ya kasance wani dandanlin kai hare haren bama-bamai kan masu adawa da Syria, ciki har da tsohon FM Rafik Hariri wanda aka kashe a cikin watan fabrairun shekara ta 2005.