An sake ganawa tsakanin wakilan Amirka da na Iran a Bagadaza | Labarai | DW | 24.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake ganawa tsakanin wakilan Amirka da na Iran a Bagadaza

Wakilan Amirka da na Iran sun sake ganawa da juna a birnin Bagadaza na kasar Iraqi akan tabarbarewar halin tsaro a wannan kasa. Jakadun kasashen biyu a Iraqi ne suka jagorancin tattaunawar. A cikin watan mayu jami´an kasashen biyu wadanda ke gaba da juna sun gana a karon farko cikin shekaru kusan 30. Amirka na zargin Iran wadda ke bin darikar shi´a da taimakawa masu ta da kayar baya a Iraqi. To sai dai gwamnati a birnin Teheran ta yi watsi da wannan zargi inda a na ta bangaren ta yi korafin cewa mamayen da Amirka ta jagoranci yiwa Iraqi ya janyo tashe tashen hankula da ake fuskanta tsakanin ´yan shi´a da´yan sunni. Ba´a tabo batun shirin nukiliyar Iran a ganawar da aka yi a Bagadaza ba. A ci-gaba da tashe tashen hankula a Iraqin kuma a yau mutane akalla 26 galibi mata da kananan yara sun rasu sannan fiye da 60 sun jikata a wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da wani asibitin yara dake birnin Hilla.