An sake ceto dubban bakin haure a Italiya | Labarai | DW | 03.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake ceto dubban bakin haure a Italiya

Hukumomi a Italiya suka ce masu tsaron gabar ruwan kasar sun kubutar bakin haure da damar gaske wanda ke kokarin shiga Turai ta tekun Bahar Rum daga kasashen Afirka.

Masu aiko da rahotanni suka ce jiragen ruwan Italiya da na Faransa da kuma wasu da ba na hukuma ba ne suka ceto mutanen da suka haura budu 3, inda a hannu guda suka ce wasu daga cikin bakin hauren da suka tasamma goma sun rasu.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance kasashen da wadanan bakin haure suka fito ba sai da hukumomi na kokari na tantance su a wuraren da aka rigaye aka killace su bayan da aka ceto su.

Wannan hali da ake ciki na faruwa ne daidai lokacin da hukumomi ke kokarin dakile yunkurin bakin haure na shiga Turai ta teku musamman daga nahiyar Afirka wanda da dama daga cikinsu kan yi asarar rayukansu a kan hanya.