1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saci bayanan jami'an gwamnatin Jamus

Ahmed Salisu
January 4, 2019

Wadanda satar bayanai ta shafa sun hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasa Frank Walter Steinmeier da 'yan majalisu da 'yan jaridu da kuma wasu fitattun mutane.

https://p.dw.com/p/3B3Mq
Symbolbild IT-Sicherheit
Hoto: imago/photothek/T. Trutschel

Masu kutse ta intanet sun saci bayanai na 'yan siyasar Jamus tare da yadawa a shafin Twitter, wanda ya bai wa jama'a da yawa damar ganin wadannan bayanai da aka sata.Wadanda wannan lamari ya shafa sun hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasa Frank Walter Steinmeier da 'yan majalisu da 'yan jaridu da kuma wasu fitattun mutane. 

Mai magana da yawun gwamnatin ta Jamus Martina Fietz ta ce daga cikin bayanan da aka sata akwai adireshin gidajen 'yan siyasa da lambobin waya da katunan shaidar zama dan kasa da na banki da sauran muhimman bayanai. Sai dai ya zuwa yanzu ba wata shaida da ke nuna cewar an saci muhimman bayanai daga ofishin shugabar gwamnatin kasar.

A cikin watan Disambar da ya gabata ne aka saci bayanan kana aka yadasu. Sai dai labarin bai bayyana ba, sai a farkon wannan makon da muke ciki.