1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace 'yan Koriya ta Kudu su uku a gabar kogin Ghana

Zulaiha Abubakar
March 31, 2018

Kasar Koriya ta Kudu ta sanar da ci gaba da kokarin nemo masu garkuwa da mutane da suka sace 'yan kasarta su uku yayin da suke tsaka da aikin kamun kifi a kusa da tekun Ghana.

https://p.dw.com/p/2vJEQ
Südkorea PK Moon Jae-in
Hoto: Reuters/Jung Yeon-Je

Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu ya bayyana cewar masu garkuwa da mutanen sun sace jirgin ne da fari tun a ranar talatar da ta gabata kafin daga baya su juya akalarsa zuwa yankin ruwayen Najeriya inda daga bisani suka kwashe mutanen uku.

A halin yanzu dai gwamnatin kasar Koriya ta Kudun ta bayayana cewar ta gaza gano in da wadannan mutane suke duk kuwa da cewar shugaban kasar Moon Jae-in ya bada dokar kar ta kwana ga ma'aikatar harkokin wajen kasar kan ta yi duk mai yiwuwa don gano inda mutanen uku suke tare kuma da dawo dasu kasar.

A nata bangaren kasar Ghana tare da hadin gwiwa da kasashen Najeriya da Togo da kuma Amirka da kungiyar Tarayyar Turai sun dukufa aikin nemo wadannan mutane da kuma wadanda suka yi garkuwar dasu.