An sace wata yar jarida a Najeriya | Labarai | DW | 23.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace wata yar jarida a Najeriya

Wasu ' yan bidiga ne suka sace yar jaridar a garin Akur da ke cikin jihar Ondo a yankin kudu maso yammancin Najeriya.

An ba da rahoton cewar wasu mutane ɗauke da makamai sun yi awun gaba da wata yar jaridar da ke gabatar da shiri a gidan talabijin na gwamnatin ƙasar. Yar jaridar mai suna Olubunmi Oke, wada ke gabatar da shiri a gidan talabijin na NTA, mutanen sun tafi da ita ne bayan saukar ta daga aiki a cikin motarta.

Babban sakataren ƙungiyar yan' jaridu na ƙasar Shu'aibu Usman Leman, ya tabbatar da cewar su na ƙokarin ganin an sako yar jaridar. A ranar Juma'a da ta gabata ma, wasu yan bindigar sun kai hari akan wani gidan kurku da ke a garin Ganye cikin jahar Adamawa, wanda suka fasa gidan yarin. Abin da ya ba da damar tserewar pursunonin, kana daga bisani suka fasa bankuna suka kwashi ganima.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Usman Shehu Usman