An sace wasu ′yan kasar China a Kamaru | Labarai | DW | 17.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace wasu 'yan kasar China a Kamaru

Wasu da ake zato 'yan Boko Haram ne sun kai hari yankin arewacin Kamaru inda suka hallaka dan kasar China daya da garkuwa da wasu

'Yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari yankin arewacin Kamaru tare da hallaka wani ma'aikaci dan China, yayin da wasu 10 suka bace kuma ake kyautata zaton an yi garkuwa da su.

Harin na daren wannan Jumma'a da ta gabata an kai a Waza mai iyaka da Najeriya, inda Boko Haram ta saba kai hare-haren da ke hallaka mutane. Lamarin ya faru dai dai lokacin da shugabannin kasashen yankin ke taro a birnin Paris na kasar Faransa domin duba hanyoyin da za a kawo karshen rikicin da ake dangantawa da tsageru masu kaifin kishin addinin Islama na kungyiar Boko Haram, tare da kubutar da 'yan mata fiye da 200 da 'yan kungiyar ke garkuwa da su.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya sadu da shugabannin kasashe makwabta bisa gayyatar Shugaban Faransa Francois Hollande.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar