Shugaban Guinea-Bissau ya rusa majalisar dokoki
December 4, 2023Dama dai ana zaman tankiya tsakanin Shugaba Embalo da gamayyar kungiyoyin 'yan adawa masu rinjaye a majalisar dokokin Guinea Bissau. An ayyana Embalo, tsohon janar din soja a matsayin wanda ya lashe zaben watan Disamba da aka je zagaye na biyu. Ya kuma tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulki a watan Fabrairun 2022.
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin mako daya da sojoji ke yunkurin kwace mulki ciki har da wanda da bai yi nasara ba a kasar Saliyo, matakin da ke zama barazana ga yammacin Afirka da ta fuskanci juyin muli a kasashe Takwas daga 2020, ciki har da Nijar da Gabon a shekarar 2023.
Kungiyar tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ta ECOWAS, ta yi tir da faruwar lamarin ta kuma jadda da goyon bayanta don kare gwamnatin dimukuradiyya.