1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe makarantun sakandare a Yobe

July 8, 2013

Mummunan harin da aka kai wata makaranta a Yobe da ke arewacin Najeriya ya sanya hukumomin jihar yanke shawarar rufe daukacin makarantun sakadaren da ke jihar.

https://p.dw.com/p/193Zu
Hoto: picture-alliance/dpa

Mahukuntan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya sun ba da sanarwar rufe dukannin makaruntun sakandaren da ke jihar daga wannan Litinin din, biyo bayan kisan wasu dalibai da malaminsu da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi ranar Asabar din da ta gabata a wata makarantar kwana.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fidda ta ce gwamnatin ta ce ba za a sake bude makarantu sakadare a jihar ba har sai an fara sabon zangon karatu cikin watan Satumbar da ke tafe.

Harin dai na makon na jiya ya yi sanadiyyar rasuwa dalibai ashirin da biyu da kuma malami guda lokacin da wasu 'yan bindiga su ka yi wa makarantar tsinke su ka jefa abubuwan fashewa kafin daga bisani su su fara harbi irin na kan mai uwa da wabi.

Wanda su ka shaida faruwar lamarin sun ce wasu daga cikin daliban da su ka rasu sun kone kurmus da ransu, batun da kungiyoyi na kare hakkin bani adama da ke ciki da wajen kasar su ke cigaba da yin Allah wadai da shi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe