An rufe jaridar Zaman a Turkiyya | Labarai | DW | 05.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rufe jaridar Zaman a Turkiyya

'Yan sanda a Turkiyya sun rufe wata jarida watau Zaman wacce ke kusa da 'yan adawar kasar.

'Yan sanda a ƙasar Turkiyya sun yi amfani da barkono tsohuwa da kuma kulake,wajen tarwatsa wasu jama'ar da suka yi dandanzo a bakin wata jaridar mai sunan zaman waɗanda jama'ar suka so su hana 'yan sandar rufe jaridar.

Kotu dai ta ba da umarni da a rufe jaridar wacce ake bugawa sati-sati.Gwamnatin Turkiyyar na zargi jaridar da haɗa baki da wani ɗan siyasar wani shehin mallami mai wa'azi da ke hijira a Amirka da nufin tayar da fitina a ƙasar.To sai dai da yake mayar da martanin babban editan jaridar ya ce gwamnatin na takura musu sakamakon sukarta da suke yi a cikin sharhunan da suke rubutawa.