An rataye wani dan Najeriya a kasar Singapore | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rataye wani dan Najeriya a kasar Singapore

Da safiyar yau din nan ne a kasar Singapore aka rataye wasu yan Afrika guda biyu dayansu kuma dan Najeriya bisa laifin safarar miyagun kwayoyi.

An rataye Iwuchukwu Amara Tochi dan Najeriya mai shekaru 21 da kuma Okeke Nelson Malachy wanda bai fadi kasar daya fito ba dan shekaru 35 da safiyar yau a gidan yari na Changi duk kuwa da kiran ahuwa da shugaban Najeriya Obasanjo da kuma kungiyar Amnesty Sukayi.

Masu fafutukar kare hakkin bil dama da sun yi yajin kin cin abinci na saoi 24 tare da kwana a bakin yarin suna masu nuna goyon bayansu ga dan Najeriyar.

An kama Tochi ne da hodar iblis gram 727 wanda kudinsu zai kai dala 970,000.

Da yake maida martani bisa rokon da Obasanjo yayi firaministan Singapore Hsien Loong yace yawan hodar iblis da Tochi ya shiga da shi kasar ya isa lalata rayukan yan kasar da iyalansu da dama.

Ana sa ran kuma zaa kone gawarwakin wadannan mutane biyu.