An rantsar da sabon shugaban Ukraine | Labarai | DW | 07.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da sabon shugaban Ukraine

Bukin rantsar da Petro Poroshenko na zuwa ne a daidai lokacin da ake fatan gano bakin zaren warware rikicin siyasa da ya jagoranci sabani tsakanin Kiev da Moscow.

A wannan Asabar din ce aka rantsar da sabon shugaban Ukraine Petro Poroshenko. Bukin rantsar da hamshakin mai kudin kasar mai kayan kwalam na zuwa ne, a daidai lokacin da ake fatan gano bakin zaren warware rikicin siyasa da ya jagoranci sabani tsakanin Kiev da makwabciyarta Moscow.

An gudanr da bukin rantsar da Poroshenko a majalisar dokokin kasar da ke Kiev, yini guda bayan ganawarsa da shugaba Vladimir Putin, a bukin cika shekaru 70 da saukar sojojin hadin gwiwa a Faransa lokacin yakin duniya na biyu.

A bayyanarsa a gidan talabijin na Ukraine bayan ganawarsa da Putin, Poroshenko ya ce an fara tattaunawa, kuma akwai fatan warware wannan rikici ta hanya madaidaiciya. Ya kara da cewar a wannan lahadi ce, wakilan kasar ta Rasha za su je Ukraine a matsayin matakin farko na cimma warware rikicin da ke tsakanin makwabtan kasashen.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu