1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon shugaban kasar tsibirin Zanzibar

November 2, 2005

Shagulgulan bikin rantsar da shugaban kasar tsibirin Zanzibar

https://p.dw.com/p/BvUX
Hoto: AP

A yayin da yake karbar rantsuwa shugaba Amani karume ya yi alkawarin gudanar da aiki ga alúmar kasar Zanzibar ba tare da nuna banbanci ba. Kana ya yi adduá ga Allah ya bashi ikon yin yiwa jamaár kasar jagoranci na gari bisa Adalci da Amana. Bikin rantsuwar ya sami halartar jakadu daga makwabtan kasashe ciki kuwa har da shugaban kasar Tanzania Benjamin Mkapa. Zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a ranar Lahadin nan data gabata ya haifar da tarzoma da tashe tashen hankula a kasar inda a kalla mutum daya ya rasa ransa wasu mutane 33 kuma suka sami raunuka a yayin dauki ba dadi tsakanin jamián tsaro da magoya bayan jamiyar Civic United Front ta yan Adawa. A Sakamakon da hukumar zaben kasar ta baiyana a ranar Talata nan, ta sanar da cewa Karume na jamiýar Juyin juya hali ta CCM wanda kuma har ila yau shi ne shugaban kasar mai ci ya sami kashi 53.2 cikin dari na adadin kuri´un da aka kada yayin da abokin hamaiyar sa Seif Sharif Hamad na jamíyar CUF ya ke da kashi 46.1 na yawan kuriún.

Ita dai jamíyar CCM ta shugaba Karume ta shafe tsawon shekaru 40 tana rike da ragamar shugabancin kasar ta Zanzibar. A waje guda dai dan takarar jamíyar Adawa Seif Sharif Hamad wanda ya sha kaye ya kauracewa bikin rantsar da sabon shugaban kasar inda kuma ya yi kira ga daukacin magoya bayan sa su gudanar da gagarumin gangami kamar yadda aka yi a kasar Ukrain domin nuna rashin amincewar jamíyar su da abin da suka kira zuren kuriú da murdiya wadda ta kai ga kwace musu nasarar da suka ce jamíyar su ta samu. A dai halin da ake ciki an tsaurara matakan tsaro a ko ina a tsibirin na Zanzibar musamman ma dai a tsakiyar birnin, yayin da a waje guda yan jamíyar Adawar suka gwammace zama a cikin gidajen su da kuma Hedikwatar jamiyar su domin gudun kada jamián tsaro su yi awon gaba da su. Ya zuwa wannan likaci dai babu rahoton wata tarzoma ko kuma tashe tashen hankula a yankin. Sai dai kuma rahotanni na cewa a yankin Pemba daya daga cikin kananan yankuna a tsibirin na Zanzibar wani maáikacin agaji ya ruwaito cewa yan sanda sun bindige wani dan jamiýar CUF har lahira, to amma yan sanda sun ce basu da masaniya akan wannan batu dama zargin da jamiyar adawar ta CUF ta yi cewa an kashe biyar daga cikin magoya bayan ta. A bangare guda dai jamian kungiyar gamaiyar Afrika dana kungiyar Commonwealth ta kasashe renon Ingila da kungiyar raya kasashen kudancin Afrika da kuma wakilai daga Amurka wadanda dukkanin su suka lura da yadda zaben ya gudana sun baiyana gamsuwa da cewa an dan sami cigaba fiye da yan shekarun baya.

Masu sa idanun sun baiyana takaici tare da nuni da da yin amfani da karfi da yan sanda suka yi a wajen zaben wanda suka ce ko kadan bai dace ba. A dangane da wannan maáikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci gudanar da bincike domin tantance zargin cewa na tafka magudi a zaben. Bugu da kari jamiyar CCM ita ce kan gaba da yawan yan majalisun dokoki a zaben na ranar lahadi kamar yadda sakamakon hukumar zaben ya nunar.