An rantsar da sabon gwamna a Kaduna | Labarai | DW | 16.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da sabon gwamna a Kaduna

A Lahadin nan ce (16.12.2012) aka rantsar da Alhaji Muktar Ramalan Yero a matsayin sabon gwamnan jihar Kaduna biyo bayan rasuwar tsohon gwamnan.

Fußball als politische Inszenierung - Kadunas Vizegouverneur Alhaji Ramalan Yaro Aufnahmeort: Kaduna, Nigeria Aufnahmedatum: 28.11.2012 Rechte: Der Fotograf (Adrian Kriesch) ist freier DW-Mitarbeiter, Rechte damit geklärt.

Fußball als politische Inszenierung - Kadunas Vizegouverneur Alhaji

Tsohon gwamnan na Kaduna dai Sir Patrick Ibrahim Yakowa ya rasu ne a jiya Asabar (15.12.2012) bayan da jirgin da ya ke ciki shi da tsohon mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Janar Andrew Azazi ya yi hadari da su a jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta.

Jim kadan bayan kammala rantsuwar kama aiki, sabon gwamnan na Kaduna ya sha alwashin dorawa daga inda marigayi Patrick Yakowa ya tsaya da nufin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma cigaba mai ma'ana a jihar.

Alhaji Mukhtar Ramalan Yero dai ya kasance mataimakin gwamnan jihar ta Kaduna kafin rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman